11 Mayu 2025 - 21:57
Source: ABNA24
Kungiyoyin Gwagwarmaya: Ajiye Makamin Gwagwarmaya Ba Zai Taba Faruwa Ba

Muhammad Al-Hindi, mataimakin babban sakataren kungiyar Islamic Jihad: Gaba da gabar yaki ba za ta saki fursunonin Isra'ila ba, sai dai idan an tsayar da yakin Gaza. Sanna ajiye makamin gwagwarmaya na nufin fara gudun hijirar Falasdinawa daga Gaza, kuma hakan ba zai taba faruwa ba.

Kamfanin dillancin labaran kasa da kasa na Ahlulbaiti (as) - ABNA - ya habarta cewa: Batun kwance damara da ajiye makami ita ce babbar matsalar da 'yan mamaya ke fuskanta, kuma gwagwarmaya da al'ummar Palastinu sun yi watsi da wanna batu gaba daya suna masu cewa tabbas ba zai taba faruwa. Ta'addancin da ake yi a Gaza da Yammacin Gabar Kogin Jordan na iya zama tamkar nasara ce ta dabara ga Netanyahu, amma suna kan wuta a tsammanin suna kan toka.

Hamas ita ma ta ci gaba da jajircewa wajen adawa da kwance damarar gwagwarmaya da sharuddan musayar fursunoni.

Muhammad Al-Qaiq, marubuci kuma manazarcin siyasa, ya bayyana a wata hira da ya yi da kafar yada labarai ta Al-Aqsa cewa: Lokacin da dakarun Qassam suka zaba don fitar da bidiyon fursunonin ya zo daidai da tattaunawar, inda suka aike da sako ga gwamnatin Isra'ila cewa lokaci ya kure. Kungiyar Hamas dai ta yi adawa da kwance damarar gwagwarmayar Palasdinawa tare da ci gaba da yin aiki da sharuddan ta na cimma yarjejeniyar musayar fursunoni.

Your Comment

You are replying to: .
captcha